Fada ya sake barkewa tsakanin marikitan kasar Somalia | Labarai | DW | 21.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fada ya sake barkewa tsakanin marikitan kasar Somalia

Duk da shirin komawa ga shawararin samar da zaman lafiya a Somalia har yanzu ana ci-gaba da gwabza fada tsakanin sojojin sa kai na ´yan Islama da dakarun gwamnatin wucin gadi dake samun daurin gindin kasar Ethiopia. Kwana na biyu a jere, sassan biyu sun yi ta harba rokoki tare da amfani da bindigogin atileri akan juna a kusa da garin Baidoa. A jiya mai shiga tsakani na KTT Louis Michel ya ce sassan da ke rikici da juna sun nuna shirin komawa kan teburin yin sulhu don samar da zaman lafiya.