Fada ya sake barkewa a Mogadishu | Labarai | DW | 29.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fada ya sake barkewa a Mogadishu

Rahotanni daga kasar Somalia sunce akalla mutane 10 ne suka rasa rayukansu cikin wani kazamin fada tsakanin dakarun kasar Habasha da wasu yan bindiga a kudancin birnin Mogadishu a safiyar yau alhamis.

Wakilin kanfanin dillancin labaru na AFP yace yaga gawarwakin wasu fararen hula 2 yayinda wadanda suka ganewa idanunsu kuma suka sanarda cewa akwai wasu mutane 3 da suka rasa rayukansu cikin wannan fada.

Wannan fada shine na farko tun ranar juma a,bayanda aka cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin dakarun Habasha dana yan kabilar Hawiye da suke riki da birnin.

A daren jiya laraba ne dai dakarun Habasha suka shiga yankin kudancin Mogadishu.