Fada ya rincabe a wasu sassan kasar Siriya | Labarai | DW | 09.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fada ya rincabe a wasu sassan kasar Siriya

Amirka da Rasha na kokarin farfado da shirin tsagaita wuta a Siriya a lokacin da ake fada a birnin Aleppo da kewaye.

Dakarun gwamnatin Siriya da kawayensu sun fafata da 'yan tawaye a kusa da birnin Aleppo a wannan Litinin. Wasu jiragen saman yaki kuma sun yi barin wuta kan wani gari da ke kusa inda 'yan tawayen suka kwace, inji wata kungiya da ke sa ido kan rikicin kasar. Yanzu haka dai rikicin ya sake rincabewa duk da kokarin da kasashen duniya ke yi na rage yawan tashe-tashen hankula. Kasashen Amirka da Rasha da ke goyon bayan bangarori dabam-dabam da ke gaba da juna a yakin basasar, sun ce za su yi aikin farfado da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma cikin watan Fabrairu, wadda ta kawo saukin fadace-fadacen a wasu sassan kasar tsawon makonni.