Fada ya kazanta a wasu sassa na kasar Sri Lanka | Labarai | DW | 10.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fada ya kazanta a wasu sassa na kasar Sri Lanka

Wasu da ake zargi ´yan tawayen Tamil Tigers ne a Sri Lanka sun harbe jami´an tsaro su hudu da kuma wasu ma´aikata 4 na wani gidan dabbobi har lahira. Bugu da kari rahotanni sun shaidar da cewa fada ya kazance a wasu yankuna na wannan tsibiri, to amma babu rahotanni kan wadanda suka jikata. Fadan da yayi tsamari a gabashin kasar ta Sri Lanka ya tilasta dubun dubatan fararen hula tserewa daga yankin. Rundunar sojin Sri Lanka ta ce a ranar juma´a kadai, mutane sama da dubu 13 suka tsere daga wuraren dake karkashin ikon ´yan tawayen Tamil Tigers zuwa yankunan dake hannun gmwanati. Kimanin mutane dubu 4 aka kashe tun bayan barkewar fadan a cikin watan desamban shekara ta 2005 duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da sassan biyu suka cimma shekaru 5 da suka wuce.