1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fada ya barke arewacin Kongo

August 30, 2007
https://p.dw.com/p/BuCk

Dubban fararen hula ne suka fara tserewa daga mummunan fada daya barke a arewacin Jamhuriyr Demokrdiyar Konko a tsakanin dakarun gwamnati da sojoji da sukayi tawaye.Wasu mayaka 1000 da suke goyon bayan janar Nkunda dan kabilar tutsi sun kai hari kann sojojin Kongo a hedkwatarsu dake Katale kusa da birnin Goma.

Sun kuma yi musayar wuta na fiye da saoi 6.wani komandan soji a arewacin Kivu kanar Delphine ya fadawa reuters cewa sun fara daukar matakai da suka dace na kawo karshen aiyukan sojojin tawaye a kasar.Jamian sojin basu baiyana yawan wadannan suka jikkata ko suka rasa rayukansu cikin wannan fada na yau ba,amma mazauna yankin sunce kusan mutane 10,000 akayiwa harbin kann mai uwa da wabi haka kuma dukkanin jamaar yankin sun tsere .