1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fada tsakanin dakarun kungiyoyin musulmi dana gwamnati

Dakarun soji dake marawa gamayyar kungiyoyin musulmi baya a Somalia sunyi arangama da na bangaren gwamnatin rikon kwarya,wadanda keda goyon bayan dakarun kasar Habasha,yini guda bayan cikan waadi adangane da janyewar dakarun kasar Habasha daga cikin somalian dake fama da rigingimun cikin gida.Tuni dai kungiyar gammayar musulmin ta bawa dakarun habashan zabin ficewa daga kasar ko kuma su fuskanci bakin daga.Jamian maaikatar tsaro na somalian dai sun tabbatar da wannan arangama ,sai babu bayanai adangane da irin asara da akayi.Wannan sabon fada dai ya barke ne a yankin Idale dake zama cibiyar kasuwanci,mai tazarar km 250 yankin arewa maso yammacin Mogadisho.