Faɗuwar kuɗin Euro | Labarai | DW | 18.05.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Faɗuwar kuɗin Euro

Ƙasashen Turai sun fara ɗaukan gagarumin matakai don ceto darajar ƙudin Euro.

default

Ƙwadola ɗaya ta Euro

Ƙasar Jamus tana matsawa takwarorin ta masu anfani da kuɗin euro, da su gaggauta cike giɓin kasafin kuɗin dake kansu, don ceto darajar takardar ta euro, wanda rigimar ƙasar Girka ta yiwa lahani. Ministan kuɗin ƙasar Wolfgang Schäuble ya shaidawa masu aiko da rohotanni a taron ministocin da ake yi a Burassel cewa, cike giɓin shine kaɗai ko wacce ƙasa za ta yi, ta ceci kanta da sauran ƙasashe. A jiya dai darajar kuɗin euro ta yi faɗuwar da bata yi ba tun shekaru huɗu da suka gabata. Shugaban ƙungiyar ƙasashen da ke anfani da kuɗin euro Jean-Claude Juncker, yace ya damu sosai yadda faɗuwar euron yake ƙaruwa kamar wutar daji.

Maqwallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu