Faɗuwar jirgi a Pakistan | Labarai | DW | 29.07.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Faɗuwar jirgi a Pakistan

Ƙasashen duniya suna ci gaba da aika saƙon ta'aziya ga al'ummar Pakistan, bisa faɗuwar jirgin sama inda aka yi asaran rai da yawa

default

Masu aikin ceto kan tarkacen jirgin sama a Pakistan

Sakatare janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki-moon ya aika da saƙon ta'aziya ga gwamnatin ƙasar Pakistan, bisa faɗuwar jirgin sama wanda ke ɗauke da fasinjoji 152. Ban Ki-moon yace abun takaici ne, yadda jirgin ya faɗi kusa da babban birnin ƙasar Islamabad, kuma ya hallaka ɗaukacin fasinjoji dake cikinta. Ƙasar Pakistan tana zaman makoki a yau alamis, bisa bala'in da shine mafi asaran rai a tarihin ƙasar na faɗuwar jirgin sama. Shaidun gani da ido suka ce jirgin wanda ya taso daga birnin Karachi izuwa Islamabad, sun hange shi yana tafiya ƙasa ƙasa lokacin da ya tinkari filin jiragen saman da zai sauka, sai kawai suka ji ƙarar faɗuwarsa.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu