Faɗan da ake yi a gabashin Kongo ya tilasta dubban mutane tserewa | Labarai | DW | 04.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Faɗan da ake yi a gabashin Kongo ya tilasta dubban mutane tserewa

Dubun dubatan ´yan gudun hijirar Kongo sun tsere zuwa kasar Uganda makwabciya sakamakon fafatawar da ake yi tsakanin sojojin gwamnati da wasu bijirarrun dakarun a lardunan dake gabashin Kongo. Hukumar kula da ´yan gudun hijira ta MDD UNHCR ta ce ´yan gudun hijirar sun shaida mata cewa suna kauracewa fadan da ake yi tsakanin sojojin gwamnati da sojojin ´yan tawaye karkashin jagorancin Janar Laurent Nkunda. Jami´an Kongo sun ce sun kashe sojoji 28 maasu biyayya da janar Nkunda, wanda ya bijirewa rundunar sojin kasar. Hukumar UNHCR ta nuna damuwa cewa dubban mutane zasu yi asarar yankunan na asali idan aka ci-gaba da gwabza fadan.