Faɗa tsakanin dakarun Sri Lanka da Tamil Tigers | Labarai | DW | 23.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Faɗa tsakanin dakarun Sri Lanka da Tamil Tigers

Rahotanni daga kasar sri Lanka na nuni dacewar,an gwabza fada tsakanin dakarun gwamnati da yan tawayen Tamil Tigers ,a yankin arewacin kasar ,wanda ya haddasa mutuwan mayakan da dama.Ɓangarorin biyu dai sun bada saɓanin rahotanni adangane da wadanda suka mutun.Jamian tsaron Sri Lankan dai sun sanar da kashe mayakan tawayen 22,bayan cafke ɗaya daga cikin matsugunnensu,tare da kame wasu mayakan,sai dai tayi asarar jamiin ta guda.Su kuma ‚yan tawayen a bangarensu,sun sanar da kashe dakarun gwamnati 17,tare da raunana wasu 54.Kimanin mutane dubu 70 ne dai suka rasa rayukan su ,a yakin basasan Sri Lanka,da ɓarkewarsa a shekara ta 1983.