1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faɗa ta ɓarke a jamho'riyar Afirka ta Tsakiya

July 20, 2010

Ƙungiyar 'yan tawaye na CPJP ta kai wasu hare hare a garin Biaro da ke a arewacin Jamho'riyar Afirka ta Tsakiya

https://p.dw.com/p/OPd4
Shugaban ƙasar Jamho'riyar Afrika ta Tsakiya Francois BozizeHoto: AP

Rahotanin daga jamho'riyar Afirka ta Tsakiya,sun ce  wani mumunar faɗa ya  rincaɓe a garin Biaro da ke a arewacin ƙasar tsakanin dakarun gwamnati da na ƙungiyar 'yan tawayen CPJP, a daidai lokacin da aka shirya gudanar da zaɓen shugaban ƙasa dakuma na 'yan majalisu a wannan shekara.

Masu aiko da rahotanin sun ce 'yan tawayen sun kai farmakin ne ga rundunar sojojin ƙasar a yankin,

 mako ɗaya da fara yin regista na ƙwance ɗamara dakarun 'yan tawayen a Paoua yankin da ke a arewa maso yammacin ƙasar.

da ya ke magana da kamfanin dilanci labarai na Faransa babban kwamanda dakarun na CPJP Abdullahi Hissene ya shaida cewa sun karɓi iko da garin na Biaro, sanarwa da dakarun gwamnatin suka mussunta.

Mawallafi:Abdourahamane Hassane

Edita       : Umaru Aliyu