1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU zata tura dakaru 3,000 zuwa gabashin Tchadi

October 15, 2007
https://p.dw.com/p/Bu8P

Ministocin harkokin wajen turai sun amince da tura dakarun hadaka 3,000,domin gudanar da ayyukan tabbatar da zaman lafiya a yankina gabashin Chadi a birnin Luxenburgh,ayayinda rahotanni ke nuni dacewar mutane kimanin 20 ne suka rasa rayukansu a rikicin kabilanci a yankin ,sakamakon harin da mayakan adawa dake goyon bayan tsohon ministan tsaron kasar suka kaiwa wanna yanki dake hada iyaka da sudan,ta lardin darfur.

Rikici tsakanin alummomin Tama da na Zaghawa,ya barke ne ,sakamakon kaura da mayakan kabilar Tama da sukayi aiki a karkashin tshohon ministan tsaroMahamat Nour sukayi, daga garin Guereda dake kann iyakar sudan,a makon daya gabata.Su dai mayakan dauke da makamai,sun zargi dakarun gwamnatin tschadin da yunkurin kwance musu makamai.Kawo yanzu dai babu cikakkun bayanai dangane da wannan fada na kabilanci ,sai dai akwai rahotanni dake nunar dacewa,mayakan kabilar ta Zaghawa,sunyi amfani da damar ficewar dakarun tshon Minister Nour,wajen afkawa yan kabilar ta Tama da hari.