1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Eu zata dauki mataki kan Turkiyya game da Cyprus

November 29, 2006
https://p.dw.com/p/BuZm

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel tayi maraba da matsin lambar da kungiyyar Eu kewa Turkiyya kann kasar Cyprus.

Angela Merkel, wacce ta shaidawa yan jaridu hakan a bayan fagen taron kungiyyar Nato, ta kara da nuna goyon bayan ta na daukar mataki, matukar Turkiyya taki amincewa da matakin kungiyyar ta Eu kann kasar ta Cyprus.

Kungiyyar ta EU dai na bukatar kasar ta Turkiyya bude tashohin ta na ruwa ne ga kasar ta Cyprus.

Kin yin hakan a cewar kungiyyar ta Eu, abu ne daka iya kaiwa ga datse tattaunawar shigowar kasar ta Turkiyya cikin yayan kungiyyar.