1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Eu zata aike da rundunar tsaro izuwa kasar Kongo

March 7, 2006
https://p.dw.com/p/Bv5k

Babban jami´in dake lura da matakan ketare na kungiyyar gamayyar turai, wato Javier Solana yayi hasashen cewa dakarun soji na kungiyyar Eu a kalla dubu daya ne zasu gudanar da ayyukan tsaro a kasar Kongo.

Wannan aikin a cewar Solana, zai gudana ne a lokacin zaben gama gari da kasar ta Kongo zata gudanar a cikin wann an shekara ta 2006.

Mr Solana, wanda ya fadi hakan a lokacin taron ministocin tsaro na kungiyyar a kasar Austria, ya kara da cewa ana sa ran Jamus ce zata yi ja gaban tafiyar da wannan aiki.

Ya zuwa yanzu dai tuni ministan tsaro na Jamus Franz Josef Jung ya tabbatar da cewa Jamus zata shiga wannan aiki, to amma ya gaza bayanin irin rawar da Jamus zata taka a cikin wannan gagarumin aikin.

Ragowar kasashen da ake sa ran zasu shiga tawagar gudanar da wannan aiki, akwai kasashe irin su Faransa da Sweden da kuma Spain.

Kasar dai ta Kongo ta shirya gudanar da zabe ne na gama gari a watan juni na wannan shekara da muke ciki idan Allah ya kaimu.