EU za ta tura masu sa ido a zaɓen Nigeria | Labarai | DW | 16.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

EU za ta tura masu sa ido a zaɓen Nigeria

Ƙungiyar taraya turai, ta yanke shawara tura masu sa iddo a zabubuka daban-daban da za a gudanar a taraya Nigeria, a watan Aprul mai zuwa.

Dan majalisa Max Van den Berg zai jagorancin ayarin masu sa idon na ƙasashen EU, su kimanin mutun 80.

Rukunnin farko zai issa Nigeria, tun mako mai zuwa, sannan tawagar zata ci gaba da zama, har lokacin da aka bayyana sakamakon ƙarshe na zaɓen.

EU ta ware kudade kimanin Euro milions 6, domin gudanar da wananaiki.

Komshinar EU, mai kula da hulɗoɗi da ƙetare, Benita Ferrero Waldner ta nunar da cewa, zaben na da matakuar mahimanci a Nigeria, da ma ƙasashen dunia, ta la´akari da cewar, shine zakaran gwajin dafi ga ɗorewar tsarin mulkin demokradiya, a wannan ƙasa da ke matsayin jigo a nahiyar Afrika.

Sanarwar ta ƙungiyar taraya Turai ta zo bayan da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta haramtawa ɗan takara Al haji Attiku Abubakar shiga zaɓen shugaban kasa.