1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

EU za ta taimaka wa Girka magance kwararar baƙin haure

Akasarin bakin haure da ke kwararowa nahiyar turai kan yi amfani ne da ƙasar Girka wajen shiga sauran ƙasashen Turan

default

Wasu baƙin haure masu neman shiga ƙasashen Turai

Hukumar Tarayyar Turai ta ce za ta tura wata tawagar jami'an tsaron kan iyaka domin taimaka wa ƙasar Girka shawo kan kwararar baƙin haure da ke shigowa daga Turkiya. Rahotanni sun ce mafi akasarin baƙin haure da ke shigowa nahiyar Turai na amfani ne da ƙasar Girka kuma yawancin waɗanda kan shigo ta mota sun ƙaru da kimanin kashi ɗaya bisa uku a wannan shekarar. Ƙasar ta Girka ce dai ta nemi taimakon hukumar Tarayyar Turan domin shawo kan matsalar baƙin hauren wadda ta ce ta daɗe tana ci mata tuwo a ƙwarya.

Kwamishiniyar Tarayyar Turai mai lura da al'amuran cikin gida, Cecilia Maimstroem ta baiyana yadda baƙin haure ke kwararowa daga Turkiya suna shiga Girka da cewa abin damuwa ne matuƙa.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙiyasta cewa baƙin haure tsakanin 300 zuwa 400 ke shiga ƙasar Girka a kowace rana. Wannan dai shi ne karon farko da hukumar Tarayyar Turan za ta tura jami'an tsaron iyakar zuwa kan iyaka da ƙasar Turkiya, za su dai kasance a wurin ne na wani taƙaitaccen lokaci. Ita ma ƙasar Turkiya a makon da ya gabata ta yi alƙawarin ba da haɗin kai ga ƙasar Girka waje daƙile shigar baƙin hauren yayin da a na ta ɓangaren Girka za ta sassauta ba da takardar Visa ga 'yan ƙasar Turkiya.Mawallafi : Abdullahi Tanko Bala Edita : Halima Balaraba Abbas