1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU za ta hukunta kasashe kan bakin haure

March 15, 2018

Kungiyar Tarayyar Turai, ta yi barazanar daukar mataki kan duk wata kasar da ta yi biris da karbar 'ya'yanta da suke cikin kasashen Turan ba bisa ka'ida ba.

https://p.dw.com/p/2uLeN
Friedensnobelpreisträger, die EU
Hoto: Getty Images/J.Guerrero

Kungiyar Tarayyar Turai, ta za ta hukunta duk wata kasar da ke kin karbar 'ya'yanta da suke cikin kasashen nahiyar ba bisa ka'ida ba. Kungiyar ta fadi hakan ne yayin da ta sanar da shirinta na hanzarta maida bakin haure kasashen da suka fito. Babban matakin dai da Turan za ta dauka, shi ne na hana manyan jami'an diflomasiyya takardun visa na shiga kasashen.

Yayin da adadin bakin hauren da ke kutsawa Turan suka ragu cikin shekara gudan da ta gabata, kasashen sun shirya maida bakin da suka sami matsalolin takardu ne, musamman wadanda, da ma ke amfani da jabu.

Kasar Faransa ga misali, ta bayyana bacin rai ne kan yadda kasar Mali ke kawar da kai ga bukatar ta kwashe 'ya'yanta da ke wadari ba tare da izinin ba.