1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

EU za ta agaza wa Pakistan

Ƙungiyar Tarayyar Turai(EU) za ta gudanar taron karo-karon taimaka wa Pakistan

default

Jose Manuel Barroso, shugaban hukumar zartarwar EU.

Ƙungiyar Tarayyar Turai(EU) na shirin gudanar da taron yin karo-karo, domin tallafa wa ƙasar Pakistan da ke cikin mawuyacin hali sakamakon ambaliyar da ta rutsa da ita. Ranar Talata ne shugaban hukumar zartarwar ƙungiyar, Jose Manuel Barroso ya ba da shawarar gudanar da wannan taro domin samar da kuɗaɗen sake gina ƙasar ta Pakistan. A dai halin yanzu, a cewar ministan harkokin wajen Pakistan, Shah Mahmood Qureishi dadaɗɗiyar abokiyar faɗan Pakistan wato Indiya, ta ci alwashin ba da agajin gaggawa na dala miliyan biyar. Al'umar ƙasar ta Pakistan miliyan shida da ambaliyar ruwan ta shafa ne, aka ƙiyasce suna zaman jiran ɗaukin abinci da tsabatattacen ruwan sha, sakamakon rashin hanyoyin kaiwa ga wannan yanki da jiragen sama masu saukar ungulu. Hukumar kula da 'yan gudun hijira da shirin abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya sun ce, mawuyacin halin da al'umar ke fama da shi ba ya misaltuwa. Ƙwararrun aikin kiwon lafiya sun yi kashedi game da fuskanatar ƙarin mace-mace, sakamakon cututtukan gudawa da amai da typhoid da kuma hepatitis.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Umaru Aliyu