1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU tayi kira da a saki yan adawa a Belarus

Zainab A MohammadMarch 26, 2006
https://p.dw.com/p/Bu7E

Kungiyar gamayyar Turai EU tayi kira ga sauran takwarorinta na turai dasu hade kai wajen bayyana adawansu da irin matakai masu tsanani da gwamnatin Belarus take dauka wajen yakan yan adawa dake zanga zanga da sakamakon zaben shugaban kasa daya gudana a ranar lahadin daya kamata.Tun a jiya nedai yansandan kwantar da tarzoman kasar suka cafke shugaban Adawa Alexander Kozulin.Mako guda kenan yan adawan Belarus din ke gudanar da wannan bore nasu,a kowace rana.Austria dake rike da kujeran shugaban EU na yanzu ta bayyana damuwanta da wannan hali da kasar ke ciki,tare da kira da a saki shugaban yan adawa dake tsare da sauran magoya bayansa.Bugu da kari Austria tayi kira ga sauran kasashen ketare da makwabtan Belarus dasu taimaka wajen kira gareta data dakatar da wannan cin zarafin yan adawa da takeyi.yazuwa yanzu dai kungiyoyin kare hakkin jamaa na kasar sun bayyana cewa akwai yan adawa guda 100 dake tsare a hannun jamian tsaro.Boren dai na adawa da ta zarce a karo na ukun shugaba Alexander Lukashenko,daga zaben daya gudana ranar 19 ga wannan wata.