Eu tayi bayani dangane da korar jakadanta a Sudan | Labarai | DW | 24.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Eu tayi bayani dangane da korar jakadanta a Sudan

Hukumar gudarnawa na kungiyar tarayyar turai ta bayyana cewa tana kokarin warware batutuwa da hukumomin kasar Sudan,adangane da korar babban jakadanta na khartum da gawamnatin kasar tayi a jiya.Kakakin hukumar Antonio Machan ta fadaw manema labaru a Brussels cewa sun samu sakon daga gwamb´natin shudan adangane da korar jamiin nasu,amma a halin yanzu suna kokarin warware wannan matsala.A jiya nedai gwamnatin Sudan ta sanar da koran wakilin na EU Kent Degerfeld da takwaransa na kasar canada Nuala Lawlor,adangane da abunda ta bayyana da tsoma bakinsu cikin harkokin cikin kasar.A dai ganin cewa wannan mataki da Khartzum ta dauka zai dada lalata dangantakar da ayanzu ke fuskantar rauni,tsakaninta da kasashen yammaci na turai,wadanda ke sukan lamirinta dangane da rikicin lardin Darfur.

Karamin ministan harkokin cikin gida na Sudan Ali Karti yace manyan jamian diplomasiyyan biyu,suna hulda da yan tawaye,wanda hakan ya sabawa gwamnatin kasar.