Eu tayi Allah wadai da Matakin da Iran ta dauka akan Israela | Labarai | DW | 27.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Eu tayi Allah wadai da Matakin da Iran ta dauka akan Israela

Kungiyyar hadin kann turai, wato Eu tayi Allah wadai da bayanin da shugaban kasar iran Ahmadinajad yayi da cewa ya kaucewa tsari na zaman lafiya.

A dai jiya laraba ne shugaban na iran yace kamata yayi a shafe kasar israela daga taswirar duniya.

Bugu da kari kungiyyar ta Eu taci gaba da cewa wannan furici babu abinda zai haifar illa yamutsi da kuma rigingimu.

Tuni dai kasashen Jamus da Biritaniya da Faransa da Spain da Belgium da Holland suka bukaci bayanin gaggawa game da wannan furuci daga ofishin jakadancin kasar ta iran dake kasashen nasu.

A waje daya kuma kasar Russia dake da alaka ta kut da kut da kasar ta iran , itama tayi Allah wadai da wannan furuci daya fito daga bakin shugaban kasar ta iran.

Ita kuwa kasar israela cewa tayi kamata yayi a soke wakilcin kasar ta iran a Mdd.