EU ta yi barazanar katse hulda da Burundi
February 15, 2016Talla
Kungiyar Tarayyar Turai ta sanar da aniyarta ta daukan matakan da suka dace kan kasar Burundi a wani mataki na bada amsa ga tashe-tashen hankulan da ke gudana a kasar. Ana ganin cewar matakan za su hada da ka katsewar duk wata gudunmawa da kungiyar ke bayarwa ga kasar ta Burundi.
Ministocin harkokin wajen kungiyar ne dai guda 28 suka sanar da wannan labari a wannan Litinin cikin wani kundi da suka amince da shi wanda kuma za' a kara tabbatar da shi ya zuwa karshen watan nan ta Fabirairu. Kungiyar ta Tarayyar Turai da ke a matsayin ta kan gaba wajen tallafa wa kasar ta Burundi na shirin katse duk wata hulda da ita tare da dakatar da tallafin da take bayarwa wanda na shekara ta 2015 zuwa 2020 suka tashi miliyan 430 na Euro.