EU ta karawa Iran wa´adin makonni biyu don kawo karshen shirinta na nukiliya | Labarai | DW | 02.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

EU ta karawa Iran wa´adin makonni biyu don kawo karshen shirinta na nukiliya

Ministocin harkokin wajen kasashen KTT sun amince su bawa Iran karin makonni biyu don ta bayyana matsayin ta na kawo karshen shirinta na nukiliya bayan da gwamnati a Teheran ta yi watsi da wa´adin MDD na dakatar da aikin inganta uranium. A kuma halin da ake ciki ministan harkokin wajen Jamus Franz-Walter Steinmeier a yau asabar yayi kira ga Iran da ta fito fili ta nuna cewa da gaske take wajen shiga shawarwarin akan dakatar da aikace aikacen ta na nukiliya. A wani labarin kuma shugaba Mahmud Ahmedi Nijad a yau asabar ya sake jaddada cewa Iran zata tsaya tsayin daka don kare manufofinta na shirin nukiliya a kowace irin tattaunawar da za´a yi akan wannan batu. Wadannan kalaman na shugaba Ahmedi Nijad sun zo ne gabanin ganawar da za´a yi a cikin mako mai zuwa tsakanin babban jami´in dake kula harkokin ketare na kungiyar EU Javier Solana da babban mai shiga tsakanin kan shirin nukiliyar Iran Ali Larijani.