1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta jinkirta lokacin yanke shawara kan shigar Romeniya da Bulgeriya cikin Ƙungiyar.

May 17, 2006
https://p.dw.com/p/Buy3

Hukumar zartaswa ta Ƙungiyar Haɗin Kan Turai, ta jinkirta lokacin tsai da shawararta, kan amincewa da shigar ƙasashen Bulgeriya da Romeniya cikin Ƙungiyar. Wata sanarwa da hukumar ta bayar na nuna cewa, da akawi bukatar yin garambawul cikin gaggawa a ƙasashen biyu. A cikin wani rahoton da hukumar ta miƙa wa Majalisar Tarayyar Turan a birnin Starßburg, ta ce za ta yi nazarin ci gaban da ake samu a ƙasashen, wajen yi wa kafofinsu kwaskwarima don su dace da tsarin da aka shimfiɗa musu, na cancantar shiga cikin ƙungiyar .

Hukumar dai ta ce matsalar cin hanci da rashawa, ita ta fi muni a ƙasar ta Bulgeriya. A Romeniya kuma, Hukumar na bukatar kasar ne ta inganta tsarinta na karɓar haraji, sa’annan kuma ta warware wasu matsalolin da suka kunno kai a fannin nomanta.