EU ta dauki mataki kan tauye hayakin motoci | Labarai | DW | 08.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

EU ta dauki mataki kan tauye hayakin motoci

Kungiyar tarayyar EU ta zargi wasu kasashe mambobinta da hada baki da manyan kamfanin motoci wajen tauye gaskiyar hayakin da motocin ke fitarwa.

Kungiyar tarayyar Turai ta fara daukar matakin shari'a a kan Jamus da Birtaniya da kuma wasu kasashe biyar mambobinta dangane da gazawar su wajen sa ido kan almundahana a gwajin hayaki na wasu kamfanonin motoci, bayan tabargazar kwange da kamfanin Volkswagen ya yi na hayaki a motocinsa masu amfani da man diesel.

Jami'ai a kungiyar ta EU suka ce kungiyar ta damu matuka cewa, gwamnatoci na hada baki da manyan kamfanonin motoci wajen tauye gaskiyar bayanai game da gurbataccen hayaki da motocin ke fitarwa wanda kuma ke da illa ga lafiyar bil Adama.

Ana dai zargin kasashen Jamus da Birtaniya da Spain da kuma Luxemburg da rashin daukar tsauraran matakai kamar yadda kamfanin kera motocin Volkswagen ya fuskanta a Amirka.