1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

EU ta dakatar da tallafin kudi ga gwamnatin Hamas

Majalisar ministocin harkokin waje na kungiyar tarayyar turai sun zartar da kudiri na dakatar da baiwa Gwamnatin Palasdinawa karkashin jagorancin Hamas tallafin kudi. Tun da farko, hukumar tarayyar turai ta baiyana yunkurin dakatar da baiwa Hamas din tallafi saboda kin amincewa da bukatun kasa da kasa na ajiye makaman ta da kuma yarda da wanzuwar kasar Israila. Kungiyar tarayyar turan ta ce za ta yi nazarin sabbin dabaru na taimakawa alúmar Palasdinawa da gudunmawar jin kai amma ba gwamnatin Hamas ba.