1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta caccaki Trump kan yarjejeniyar Iran

Abdul-raheem Hassan
October 16, 2017

Kungiyar Taryyar Turai ta hau teburin naki a kan shirin shugaban Amirka Donald Trump, da ke neman maida hannun agogo baya a kan mutunta yarjejeniyar da kawancen kasashen EU suka cimma na cinikayya da kasar Iran.

https://p.dw.com/p/2lu2A
Luxemburg Treffen der EU-Außenminister
Hoto: Getty Images/AFP/J. Thys

Kasashe mambobi kungiyar EU, sun soki matakan shugaban Amirka Donald Trump da ke neman dakile yarjejeniyar Nukilyar Iran. A yayin wata ganawa mambobin kungiyar a Luxemburg, EU ta ce wadannan matakan ka iya haifar da tabargaza a yunkurin sulhunta wutar rikici da ke ruruwa tsakanin Koriya ta Arewa da sauran kasashen duniya kan sarrasa makaman kare dangi.

Babbar jami'ar harkokin waje na kungiyar Tarayyar Turai Federica Mogherini ta ce "Ina sa ran dukkanin mambobin kungiyar EU, za su ci gaba da mutunta yarjejeniyar ci gaba da kulla dangantaka da kasar Iran. Kada a sake a ba da fuska da yunkurin Trump, wanda ka iya rusa shirin shiga tsakani da gwamnatin Pyongyang."