Matakin binciken 'yan gudun hijira
December 16, 2015Hukumar kungiyar Tarayyar Turai a ranar Talata ta bukaci mahukunta akasar Italiya su yi amfani da karfi wajen tattara bayanai na hotunan yatsu ga baki dayan sabbin 'yan gudun hijira a kasar, bayan da ta samu kasar da laifi na rashin tattara bayanan cikin rumbun ajiyar bayanai na kasashen na EU.
A cewar hukumar kasar ta Italiya ya zame mata dole ta dauki matakan doka masu tsauri wajen tattara wadannan bayanai na 'yan gudun hijirar ko da kuwa zai sanya a tsare wadanda suka ki yarda a dauki hotunan yatsunsu tsawon lokaci. A cewar kalaman na hukumar ya zama dole a tabbatar da tattara bayanan yatsu na bakin hauren dari bisa dari ba tare da bata lokaci ba.
Ministan harkokin cikin gida a kasar ta Italiya Angelino Alfano a jiya Talata ya ce da ma tsarin dokar kasar ta Italiya ya amince da amfani da karfin sai dai 'yan majalisa na sake nazari kan wannan bukata.
A ranar Alhamis ne dai babban taron na EU zai tattauna kan sabon shiri me cike da takaddama wanda zai bayyana a wannan mako, shirin da zai ba wa jami'an tsaro dama a kan iyaka su kutsa kai cikin wata kasa da ke karkashin kungiyar ba tare da sani mahukuntanta ba.