EU ta amince da yarjejeniyar CETA | Labarai | DW | 15.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

EU ta amince da yarjejeniyar CETA

Majalisar dokokin Kungiyar tarrayar Turai ta amince da wani shirin na huldar cinikaya da ke cike da cece ku-ce tsakaninta da kasar Kanada.

Shirin da ake kira da suna CETA  wanda ya janyo zanga zangar jama'a a birnin Strasbourg na Faransa cibiyar majalisar dokokin ta tarrayar Turai gabannin kada kuri'a 'yan majalisar a kai, ya tanadi soke kudaden fito tsakanin kasashen na Turai da Kanada da kishi 99 cikin dari da kuma hulda a fanin kare muhalli da kiwon lafiya.Masu yin adawa da shirin na CETA na cewar zai janyo koma baya ga manoma a nahiyar ta Turai.