EU ta amince da daftarin ficewar Birtaniya
April 29, 2017Talla
Shugaban Kungiyar Tarayyar Turan Donald Tusk wanda ya sanar da hakan a ranar Asabar din nan a shafinsa na Twitter yace daukacin kasashe 27 na kungiyar ta EU suka amince da jadawalin a taron kolin da suka gudanar a Brussels.
Jami'ai sun ce cikin minti guda shugabannin suka amince da daftarin inda kuma suka kwashe da tafi.
Shi ma shugaban hukumar hadin kan Turai Jean Claude Juncker ya aike da sako ta Twitter yana mai cewa hadin kai ya tabbata.
Ana sa ran mashawarci kan ficewar Birtaniya daga kungiyar ta EU Michel Barnier zai fara tattaunawa kan ficewar bayan zaben majalisun dokokin da Birtaniyar za ta yi a watan Yuni.