EU ta ƙara sanyawa Iran takunkumi | Siyasa | DW | 27.07.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

EU ta ƙara sanyawa Iran takunkumi

Rasha ta yi suka ga matakin ƙarin takunkumi da ƙungiyar EU ta ɗauka akan Iran

default

Shugaban Hukumar ƙungiyar EU Herman van Rompuy tare da Kwamishiniyar harkokin waje Catherine Ashton

Kwana ɗaya bayan da ƙasashen ƙungiyar Tarayyara Turai su ka bada sanarwar ƙara kafawa Iran takunkumin karya tattalin arziki don gane da shirinta na nukiliya, Ƙasar Rasha ta bi sahun irin wajen bayyana takunkumin da cewar bazai saɓu ba wai bindiga a ruwa:

Bayan da ministocin harkokin wajen ƙasashen Turai suka kammala taronsu a jiya, sun amince da ƙara ƙaƙabawa Iran takunkumin karya mata tattalin arziki da ya shafi ciniki ta fuskar man fetur da Iskar Gas da kuma fasahohin zamani.

Dalilin ɗaukan wannan mataki dai, inji kwamishiniyar harkokin wajen ƙungiyar ta Turai, Catherin Ashton shine a sake tilastawa Iran dakatar da shirin inganta sinadaran Uranium da zai iya kaita ga ƙera makaman nukiliya na ƙare dangi. Tare kuma da sake maido da ita teburin tattaunawa tsakanin ta da wasu ƙasashen duniya shida da su ka haɗa da Amirka da Jamus da Faransa da Birtaniya da kuma Rasha.

Inda ta ci gaba da cewar:"  fatanmu shi ne dawo da Iran teburin sasantawa akan wannan batu na nukiliya. Mu na buƙatar samun bayanai da su ka shafi aiyukan farar hula na wannan shiri nata. Bayanai da zai kai ga samun fahintar juna domin wanzar da ci gaban Iran da kuma Turai ta fuskoki daban-daban"

To sai dai a martanin da ta fitar a yau Talata, kwana ɗaya bayan da ƙungiyar ta Turai ta ɗauki wannan mataki, ɗaya daga cikin  ƙasashen na duniya da ke shiga tsakanin Iran da kuma ƙasashen yamma, wato Rasha ta fitar da wata sanarwa da ke Allah wadai da matakin da ƙungiyar ta EU ta ɗauka akan Iran, sanarwar da ma'aikatan harkokin wajen Rasha ta fitar tace ko da wasa, batun ƙarin takunkumi akan harkokin makamashi da aka ce an sanyawa Iran, ba abinda da zai samu amincewar ƙasashen duniya ba ne, don haka tun dare bayi ba, ƙasashen na Turai kamata tayi su sake Tutani. Ko'a acan baya ma dai Rasha ta sha bayyana goyon bayan ta ga shirin Iran na mallakar makamashin na nukiliya domin amfanin fararen hular ƙasar, saɓanin na soji da ƙasashen Turai ke zargin Iran da ƙoƙarin ƙerawa.

To sai dai a ta bakin mataimakin shugabar gwamnatin Jamus kuma ministan harkokin waje Guido Westerwelle, shima ya jaddada yancin da Iran ke da shi na mallakar makamashin nukiliya domin amfanin fararen hula, sai dai kamar yadda yace akwai lauje cikin naɗi; Westerwelle yace "Iran ta na da cikkaken yancin samar da nukiliyan ta, amma wannan yanci na ta ba zai hana yancin da sauran ƙasashen duniya ke da shi suma na sanin matakan da Iran ke ɗauka domin sarrafawa ko mallakan wannan makamashi ba,  domin kada ta fake da guzama domin harbin karsana, domin barin Iran ta mallaki makamin nukiliya hatsari ne.

Yanzu dai bayan ƙasar Rasha da ta yi suka game da wannan mataki, itama Iran ta maida martani, Inda kakakin ma'aikatan harkokin wajen ƙasar Ramin Memanparast yace matakin na EU, matsi ne kawai daga ƙasar Amirka, wanda kuma ya maida Turan zaman 'yar amshin shatan Amirka, ta sadukar da  nata yancin da take dashi. Abinda kuma yace ba zai sa Iran ta sauya matsayin ta akan shirin na nukiliya ba.

Sabon takunkumin da ƙasashen na yanma suka sanyawa Iran ɗin dai ya shafi saye da sayarwa ta fuskar manfetur da iskar Gas da hada-hadar kuɗi da bankunan ƙasa da ƙasa. Takunkumin da tuni ƙasashe irin su Amirka da kuma Kanada suka yaba da ɗaukan sa.

Mawallafa: Christoph Hasselbach/ Babangida Jibril

Edita: Yahouza Sadissou Madobi