1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

EU: Ministoci za su gana bayan harin Brussels

Kasar Holland da ke jan ragamar shugabancin wannan kungiya ta bayyana haka a ranar Laraban nan.

Belgien Schweigeminute EU Brüssel

Jami'ai daga kasashen EU

Ministoci na cikin gida da na shari'a daga kungiyar Tarayyar Turai za su yi wani zama a ranar Alhamis a birnin Brussels na Beljiyam, abin da ke zuwa bayan kai harin da ya yi sanadi na rayukan mutane 31 kamar yadda jami'ai daga kungiyar ta EU suka bayyana a ranar Laraban nan.

Kasar Holland wacce ita ke jan ragamar wannan kungiya a mulkin da a ke na karba-karba, a sakon da ta fitar na Twitter ta ce taron zai hada ministocin na shari'a da na tsaro da wakilai daga ma'aikatu daga Kungiyar ta EU.