1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU da AU da MDD akan fadada tsaro a Darfur

Zainab A MohammadMay 25, 2005

Taron kaddamar da gidauniyar fadada harkokin dakarun tsaro a lardin Darfur a yammacin Sudan Gobe Alhamis

https://p.dw.com/p/Bvbg
Hoto: AP

A gobe alhamis ne kungiyar gamayyara Afrika ta Au ke kaddamar da gidauniyar neman agaji daga kasashen ketare domin inganta ayyukanta na samarda zaman lafiya lardin Darfur dake yammacin Sudan.

Ayayinda jagoran majalisar dunkin duniya Kofi Annan ke shirin kasancewa babban bako a taron neman agajin samar da tsaro a ladin Darfur,kungiyar gamayyar Afrika mai wakilan kasashe 53 na fatan samun tallafi mai tsoka daga kungiyar tsaro ta NATO,da kungiyar gamayyar turai EU,da Amurka da ita kanta Mdd.

Gabannin wannan taro dazai gudana a gobe alhamis,kakakin kungiyar ta kasashen Afrika Assane Ba, ya bayyana cewa a shirye suke su samarda Dakaru amma suna bukatar kayayyakin aiki da kudaden gudanarwa.

A tsarin neman taimakon dai kamar yadda kamfanin dillancin labaru na AFP yayi nuni dashi,Kungiyar ta Au na bukatar jiragen daukan dakaru da makamansu 116,da motocin ambulance ambulance na daukan jamiaan soji marasa lafiya 24 da motocin agaji,da wasu motocin daukan jamaa guda 10 kana da jiragen yaki masu kirar saukan ungulu 6.

Bugu da kari kungiyar na bukatar tallafin jiragen sama na fasinja dana daukan kayayyaki,da wasu motoci kiran pic-up pic-up,da manya da matsakaita da kuma kananan ababan hawa.Baya ga wannan Au tace tana kuma bukatar naurorin sadarwa dana office masu dunbin yawa,da suka hadar da naura mai aiki da kwakwalwa watau komputa guda 280,naurorin buga rubutu dana daukar hoto na zamani.

Abun nufi anan inji jamiin diplomasiyya na turai dake birnin adisa baba shine, kungiyar ta AU zata samarwa sojojin kayayyakin matsugunnensu dana rundunoninsu idan har takwarorinsu zasu taimaka da harkokin sufuri da kuma kudaden gudanarwa.

A jiya talata nedai kungiyar tsaro ta NATO tayi alkawarin bada agajin sufuri da horaswa a wannan kuduri da kungiyar gammayar Afrika ta sanya gaba na fadada yawan dakarun tabbatar da zaman lafiya a Lardin na Darfur daga 2,200 zuwa 7,700 a watan Satumba,kana wani lokaci nan gaba zuwa dubu 12.

Duk dacewa kungiyar tsaro ta Nato bazata bayar da agajin dakarunta wajen harkokin tsaro a Darfur ba ,a goben ne ake saran babban sakataren ta Jaap Scheffer zai sanarda gudummowansu,wanda kuma ke zama karo na farko da suka bada agaji a nahiyar afrika.

Kungiyar gamayyar turai anata bangare tayi alkawarin samarda makamai da sauran naurorin aiki da suka hadar da motoci da rumfuna .Ayayinda jamiin harkokin wajen kungiyar Javier Solana ya sanar dacewa kungiyar zata dauki nauyin jigilar dakaru daga kasashen Rwanda da Afrika ta kudu da Senegal da Nigeria zuwa lardin na Darfur.

Banda wadannan kayayyakin aiki dai kungiyar ta gammayar Afrika zata bukaci kudade masu dumbin yawa a yunkurinta na samarda zaman lafiya a lardin na darfur,inda rikicin shekaru biyu tsakanin yan tawaye da dakarun gwamnati yayi sanadiyyar asaran rayukan mutane da aka kiyasta dubu dari uku,ayayinda wasu million biyu suka tsere daga matsugunnensu.

Bayan kaddamar da wannan gudauniya na agaji wa kungiyar ta gamayyar Afrika wa Lardin na Darfur da zai gudana a gobe alhamis a birnin Adisa baban kasar Ethiopia,wanda ke zama headquatarta,ana saran babban bako kuma sakataren mdd Mr Kofi Annan zai ziyarci lardin na Darfur dake yammacin Sudan.