Eu da Amirka za su fara misayan bayyanan bankuna | Zamantakewa | DW | 29.06.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Eu da Amirka za su fara misayan bayyanan bankuna

Majalisar Turai na shirin kaɗa ƙuri'ar amincewa da yarjeniyar da EU da Amirka suka cimma game da misayan bayanan ayyukan bankuna.

default

Tutar Amirka da ta EU

Akasarin jam'iyun da ke da wakilci a majalisar dokokin tarayyar Turai sun yi alƙawarin bayar da goyon bayan da ake bukata wajen ɗage shingen da ya hana ruwa guda a musayan bayanan bankunan tsakanin Eu da kuma Amirka. 'Yan majalisa da suka yi ɗari ɗari da batun a baya, suka ce sun gano irin ci gaban da za a samu tsakanin ƙasashen 27 na EU da kuma Amirka a batun yaƙi da ta'addacin da dukkaninsu suka sa a gaba. A saboda haka ne zaman majalisa Eu ɗin da za ta yi nan da 'yan kwanaki, zai zama na albarkantar yarjejeniyar da Spain ta cimma da Amirka game da musayan bayanan da suka shafi ajiyar waɗanda ake zargi da ayyukan tarzoma. A lokacin da ta ke bayani, komishiniyar EU da ke kula da harkokin cikin gida, wato Cecilia Malmström, ta ce ta yi imanin cewa 'yan majalisan na Turai ba za su zuba musu ƙasa a ido ba:

Wechselstube mit Dollar und Euro Geldscheine

Euro da kuma dollar Amirka

" muna kyautata zaton cewa majalisa za ta bayyana matsayinta a zamanta na mako mai zuwa a Strasbourg. Na yi imanin cewa sun fahimce irin ci gaba da za a samu idan ta yi na'am da wannan yarjejeniya

A zamanta na watanni huɗun da suka gaba dai, majalisar ta Turai fatali ta yi da batun na misayen bayanan , saboda abin da ta danganta da shisshigi cikin al' amuran bayin Allah da ake neman yi. Sai dai bayar da kai domin bori ya hau da waɗanda aka zaɓa ƙarƙashin jam'iyun gurguzu da na jari hujja suka yi , ya sa ana ganin zaman majalisar kamar ta ran sarki ya daɗe ne, domin ba za a tafka wata zazzafar mahawara ba. Birgit Sippel, 'yar majalisar Turai da aka zaɓa ƙarƙashin jam iyar SPD daga Jamus ta nuna mahimmacin amincewa da yarjejeniyar:

" Za a fara tantace sahihancin zargin ayyukan da suka shafi tarzoma da Amirka za ta yi kafin a miƙa mata sirri ajiyar bankunan. Kuma abin farin ciki ma, shi ne kafin a mika mata bayanan, sai an yi la'a akari da dokokin kowacce daga cikin ƙasashen na Turai da yarjejeniyar zai shafa.

EU und USA setzen Bosnien Frist für Reformen

Tattaunawar EU da Amirka

Su dai ƙasashen na turai sun bayyana aniyarsu ta kafa wata hukuma mai zaman kanta da za ta tantance bayanan da ya kamata ta mika ma hukumomin Washington. Wannan matakin dai, zai bayar da damar jibge ɗaukacin misayan kuɗin da aka yi daga nahiyar Turai, ko kuma tsakanin bankunan na Turai. sai dai har yanzu ana ci gaba da dasa ayar tambaya game da ɓangare da za a ɗora ma wannan nauyi, imma hukumar 'yan sanda ko kuma kotun ƙasashen na Turai. Watanni shida za a shafe daga daya ga watan Agusta kafin sabuwar dokar da ta shafi miƙa bayanan ajiya ga Amirka za ta fara aiki.

Mawallafi. Mouhamadou Awal

Edita: Yahouza Sadissou