Ethiopia ta yi belin yan Sweeden 3 da ta capke | Labarai | DW | 19.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ethiopia ta yi belin yan Sweeden 3 da ta capke

Ƙasar Ethiopia, ta bada sanarwar belin turawanan nan yan ƙasar Sweeden guda 3, da ta capke, bayan ta zarge su da ayyukan ta´danci.

Gwamnati Ethiopia ta bada odar capke wannan mutane, a farkon shekara da mu ke ciki ,a lokacin da rikici ya ɓarke a ƙasar Somalia.

Jami´an leƙen asiri Adis Ababa ,sun nunar da cewa mutanen 3 na da hannu a cikin tashe-tashen hankullan da ke wakanan abirnin Mogadiscio.

Duk da kiranye-kiranye gwamnatin Sweeden, Ethiopia ta yi kunnen uwar shegu.

Har ya zuwa yanzu, gwamnati ba ta bada ƙarin haske ba a game da sallamar mutanen3.