ETA ta yi shelar ajje makamai | Labarai | DW | 05.09.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

ETA ta yi shelar ajje makamai

Ƙungiyar ´yan aware ta ETA a yankin Basque na Spain ta bayyana ajje makamai

default

ETA ta ajje makamai

Ƙungiyar ETA ta ´yan awaren yankin Basque a ƙasar Spain , ta yi  wa gwamnatin Firaminista Zapatero tayin tsagaita wuta.Wata jarida ce ta yankin Basque ɗin ta bayyana wannan labari a cikin shafin da ta buga, inda ta nuna hotunan wasu shugabanin ETA su ukku su na wannan kira.

Masu bin diddiƙin rikici tsakanin dakarun Spain da ETA, sun yi nuni da cewar Ƙungiyar ta ´yan aware ta ga uwar bari ne, domin a baya-bayan nan, haɗin gwiwar jami´an tsaron Faransa da na Spain, sun raunana ta matuƙa.

Cemma a shekara 2006 sai da ETA ta yi shelar aje makamai, amma daga bisani ta koma filin daga, tare da ɗana bam a filin saukar jiragen samar birnin Madrid,harin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyu.

Daga farko ɓarkewar rikicin  Ƙungiyar ETA a shekara 1951, kimanin mutane dubu su ka rasa rayuka daga ɓangarorin biyu.

Mawallafi: Yahouza Sadisou Madobi

EDita: Zainab Mohamed Abubakar