1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Eritrea ta bukaci majalisar Dinkin Duniya da ta kwashe yanata ta bar kasarta

Hauwa Abubakar AjejeDecember 7, 2005

Eritrean tace,jamian Amurka canada Turai da Rasha su bar mata kasarta

https://p.dw.com/p/Bu3Z

Cikin wani mataki da ake ganin zai kara shafar dangantaka tsakanin Eritrea da Majalisar Dinkin Duniya tare da tsoron sake barkewar fada a bakin iyakarta da Habasha,kasar Eritrea ta baiwa maaikatan majalisar Dinkin Duniya kwanaki 10 da su kwashi ya nasu ya nasu su bar kasar.

Cikin wata wasika da gwamnatin Eritrea ta aikewa majalisa tace,maaikatan majalisar da suka fito daga kasashen Amurka,Canada da kuma Turai,ciki harda kasar Rasha, an basu waadin kwanaki 10 da su bar kasar.

Wasikar tace wannan oda ta shafi dukkan maaikata na kasashen da aka zaiyana koda kuwa wane irin aiki suke yi a kasar ta Eritrea.

Wasikar wadda aka aika da kofinta zuwa ga kanfanin dillancin labarai na AFP,tana dauke da sanya hannun kanar Zecarias Ogbagaber,jamiin hulda na Eritrea a Majalisar Dinkin Duniya.

Yace wannan mataki an dauke shine sakamakon wata shawara da gwamnatin Eritrea ta yanke game da wasu jamian majalisar,amma bai baiyana ko wadanne dalilai ne ba.

Ba a dai tabbatar da yawan maaikata da korar ta shafa ba,amma jamian diplomasiya sunce kimanin maaikata 100 na majalisar sun fito daga kasashen da Eritrean ta nemi su bar mata kasarta.

Duk da cewa wasikar bata baiyana dalilan korar jamian majalisar dinkin duniyar ba daga Eritrea,amma akwai alamun hakan ba zai rasa nasaba da rashin jin dadi da barazanar da komitin sulhu yayi ba,na lakabawa Eritrea takunkumi har sai ta sassauta dokarta akan sintiri na jamian majalisar.

Su dai kasashen Amurka,Rasha da kasashen Turai da dama,membobi ne na komitin sulhun,wadda ta jefa kuria a ranar 23 ga watan nuwamba,tana mai barazanar dora takunkumin tattalin arziki dana diplomasiya akan Eritrea da Habasha muddin dai sun koma yaki akan bakin iyakokinsu.

Hakazalika komitin sulhun ya gargadi Eritrea cewa zata fuskanci horo na majalisar,har sai ta kawadda dokar hana sintiri ko zirga zirga ga jamian majalisar da suke aiki a kasar.

A watan oktoba daya gabata ne Eritrea ta haramtawa jirage masu saukar angulu na majalisar yin shawagi a sararin samaniyarta hakazalika ta hana jamianta yin sintiri a bakin iyakokinta da Habasha.

Tun daga wancan lokacin ne,maaikatan Majalisar Dinkin Duniya suka samu cikas ga gudanar da aiyukansu a kusan kashi 60 na yankunan da aka kebe zasu gudanar da aiyukansu a cikinsu,hakazalika sun bada rahoton zirga zirga na sojoji daga bangarorin biyu inda suka ce akwai alamar sake barkewar yaki tsakaninsu.

Kasashen Habasha da Eritrea, sun gwabza mummmunan yaki tsakaninsu daga shekarar 1998 zuwa 2000 akan batun iyakokinsu,kuma a yan watannin baya bayannan,gwamnatin Eritrea tayi gargadin cewa akwai yiwuwar barkewar wani sabon rikici saboda gwamnatin Habasha taki amincewa da yarjejeniyar da ta shata sababbin iyakokin kasashen biyu.