Erbil: Haramcin zirga-zirgar jiragen sama ya soma aiki | Labarai | DW | 29.09.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Erbil: Haramcin zirga-zirgar jiragen sama ya soma aiki

Kasashe da dama sun dakatar da zirga-zigar jiragen sama a yankin Kurdawan Iraki bayan zaben raba gardama mai cike da cece-kuce na neman ballewar yanki daga Iraki.

Irak Flughafen Erbil (Reuters/A. Lashkari)

Filin tashi da saukar jiragen sama na birnin Erbil

Tun dai kafin wannan mataki ya soma aiki baki da dama da ke yankin Kurdawan suka yi ta ficewa daga yankin, inda zirga-zirga jiragen sama na kasa da kasa ta tsaya cik awa daya kafin wa'adin da Iraki da bayar a wannan rana ta Juma'a. Wani dan yankin na Kurdawan mai suna Ali Kadir ya nuna bacin ransa kan lamarin:

"Ba mu ne muka haddasa wannan matsala ba. Matsala ce da ta taso daga gwamnatin Iraki. Mun dauki mataki ne domin inganta makomarmu, kuma 'yancinmu ne. Kamar Turkiyya da Iran, mu ma muna da 'yancin samun tamu kasar. Muna son Turkiyya da Iran su dawo a kan bakansu na janye jiragensu."

Haramcin wanda ya shafi filin jiragen sama na biranen Erbil da na Souleimaniyah, bai shafi jiragen agaji da na sojoji, ko kuma na diflomasiyya ba a cewar Talar Faiq Saleh shugabar filin jirgin saman birnin na Erbil babban birnin yankin na Kurdawan Iraki. Sai dai ministan harkokin sufuri na yankin Mawloud Bawa Mourad ya ce za su dauki matakai na ganin zirga-zirgar jiragen saman na kasa da kasa ta dawo.