Macron zai kawo sauyi a Tarayyar Turai
May 14, 2017Talla
Anasarn Macron zai tabbatar da goyon bayansa ba wai ga kungiyar ta EU kadai ba, har ma da Tarayyar Jamus, a lokacin ganawarsa da shugabar gwamnati Angela Merkel a ziyarar farko da zai kawo Berlin a gobe.
Kazalika a wannan Litinin din ce ake saran mai shekaru 39 da haihuwar, kuma tsohon ministan tattalin na Faransa, zai gabatar da sunan fraiministansa, a cewar majiya mai tushe da ke kusa da fadar shugaban kasar.
Kafofin yada labarun Faransan dai sun ruwaito rade-radin yiwuwar nada magajin garin Le Havre mai ra'ayin mazan jiya Edouard Philippe a matsayin sabon fraiministan, sai dai zaben 'yan majalisar wakilai da zai gudana a wata mai zuwa zai iya sauya komai, tunda wajibi ne jam'iyyar da ta fi rinjayen kujeru ta kasance mai kafa gwamnati.