An bai wa shugaban kasar Faransa lambar yabo
May 10, 2018Talla
Shugaban na Faransa ya samu kyautar lambar yabon ne a birnin Aachen saboda manufofinsa na samu hadin kai na kasashen Turai. Wannan lambar yabo da birnin na Aachen ke bayar da ita tun a shekara ta 1950 ga gwarzayen mutane da suke fafutuka don nahiyar Turai. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta taba samun kyautar a shekara ta 2008.