Ellen Johnson-Sirlef ta yi ikirarin lashe zaben shugaban kasar Liberia | Labarai | DW | 11.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ellen Johnson-Sirlef ta yi ikirarin lashe zaben shugaban kasar Liberia

Tsohuwar masaniyar tattalin arziki ta Bankin Duniya kuma tsohuwar ministar kudin Liberia Ellen Johnson-Sirleaf ta yi ikirarin lashe zaben shugaban kasar ta Liberia. Har in dai hakan ta tabbata to Ellen Johnson zata zama mace ta farko da aka zaba a mukamin shugaban wata kasa a Afirka. Yanzu da aka kammala kidayar kusan kashi 90 cikin 100 na kuri´un da aka kada a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar, hukumar zaben kasar ta ce Johnson-Sirleaf ta samu yawan kuri´u kimanin kashi 60 cikin 100. A halin da ake ciki babban mai kalubalanta kuma tsohon shahararren dan wasan kwallon kafa George Weah ya mika wata takardar zargin tabka magudin zabe ga hukumar zaben kasar. Shugaban tawagar MDD a Liberia ya bayyana zaben da cewa an yi shi cikin lumana kuma an kamanta adalci a ciki.