El-Beshir ya kare kansa daga zargin kissan gilla a Darfour | Labarai | DW | 24.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

El-Beshir ya kare kansa daga zargin kissan gilla a Darfour

Shugaban Sudan Omar el-Bashir, ya nemi kare kan sa daga zargin da ake masa, na saku saku da batutuwan da suka shafi rikicin Darfur, inda ya zargi kafofin yada labarai na kasa da kasa, da wuce gona da iri wajen nuna yawan mutanen da suka mutu, sanadiyar rikicin yankin na Darfur, a wani video da aka nuna jiya juma’a, a wani masallaci dake birnin Detroit na Amurka. El-Bashir yace ya tabbatar da irin wahalolin da al’uman Darfur ke ciki, amma kuma yace laifin kungiyoyin tawaye ne, wadanda suka nisanta kansu daga yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma, a watan mayun shekarar 2006 a birnin Abujan Nijeriya. Masana sun kiyesce cewar akalla, mutane dubu dari 2 suka rasa rayukan su, a yayin da wasu miliyan 2 da rabi suka rasa gidajen su a rikicin na Darfur da ya ki ci ya ki cinyewa.