El Beshir da Deby sun nemi juna gafara | Labarai | DW | 08.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

El Beshir da Deby sun nemi juna gafara

A birnin N´Djamena na ƙasar Tchad, an yi bikin rantsar da shugaban ƙasa Idriss Deby Itno, bayan zaɓen da ya lashe a watan Mayu da ya gabata.

Shugabanin ƙasashen Afrika da dama, wanda su ka haɗa da na Sudan, Umar El Bashir su ka halarci bikin.

Danganta tsakanin Sudan da Tchad, ta fuskanci ƙarin taɓarɓarewa a lokacin shirye shiryen zaɓen Tchad, inda yan tawaye su ka kai farmaki, a N´Djamena, da burin kiffar da shugaba Idriss Deby.

Hukumomin Tchad, sun zargi Sudan da tallafawa yan tawaye.

A dangane da haka, su ka yanke shawara katse hulɗoɗin diplomatia da Khartum.

Albarakacin bikin rantsar da shugaba Idriss Deby da Omare El beshir ya halarta, shugabanin kasshne Afrika sun yi anfani da wannan dama, domin shirya wani ɗan ƙwarya ƙwaryan taron ƙoli na ba zata, bisa jagorancin shugaban kasar Lybia Mohhamar Khaddafi.

A sakamakon wannan taro, Deby da Al Bahsir sun taɓa da juna, sun kuma tabbatar da cewa, nan da ɗan lokaci ƙalilan za su sake buɗa kofofin jikadancin su a N´Djamena da Khartum.

Shugabanin 2, sun bayyana ɗaukar mattakan haɗin gwiwa, domin samar da kwanciyar hankali a iyakokin su.

Saidai ƙasar Tchad, ya shawarci tura rundunar ƙungiyar tarayya Afrika, da zata kulla da wanzuwar zaman lahia a yankin.