Ehud Olmert ya shiga tsaka mai wuya | Labarai | DW | 04.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ehud Olmert ya shiga tsaka mai wuya

Kwanaki kaɗan bayan yaƙin da aka gwabza tsakanin Isra´ila da dakarun Hizbullahi , Praminista Ehud Olmert, ya shiga wani hali na tsaka mai wuya.

Bayan zargin da a ka yi masa, na taka mummunar rawa, a cikin yaƙin, yanzu kuma, komitin bin diddiƙin tattalin arzikin ƙasa ya tuhume sa, da hannu cikin wata sabuwar badaƙƙala.

Komitin ya bukaci ya buɗa bincike, na maussaman , domin gano gaskiya a kan zargin da a ka yiwa Ehud Olmert, na naɗa wasu ma ´aikata 4, ba bisa ƙa´ida ba,a lokacin da ya riƙe matsayin ministan kasuwanci da makamashi.

Komitin na kyauttata zaton, Ehud Olmert, ya bi san zuciyar sa, a lokacin da ya naɗa mutanen 4, ta la´akari da cewar, basu dace ba, ko miciƙala zaratin,a wannan wurare.

A ɗaya hannun kuma, idan ba a manta ba, a kwanakin da su ka gabata, an zargi Praminsita Isra´ila da almmudahana da dukiyar ƙasa, a sakamakon gano wani hamshaƙen gida da ya mallaka a birnin Ƙudus.