1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Egechek magoyin fata na Abzinawan Nijar

Tila Amadou | Yusuf Bala Nayaya
December 14, 2016

Egechek magoyin fata na kabilar Abzinawa na daya daga cikin al'adu na wannan kabilar da ke girmamawa a lokutan sabgoginsu na aure da haihuwa.

https://p.dw.com/p/2UG2t
Niger Tuareg mit Bauchtaschen
Hoto: DW/T. Amadou

A wajen kabilar Abzinawa har kwanan gobe masu rayuwa a karkara na amfani ne da magoyin fata wanda da Abzanci ake kira Egeche, wanan magoyin dai a kan sarrafa shi ne da fatar akuya da majema mata ke jemewa, kuma wannan magoyin a kan tanade shi musamman ma a haihuwar da amarya ta yi ta farko. Egechek magoyin yaro a wajen kabilar ta Abzinawa, 'yan gidan maza ke kawo shi, a cikin kayan barka da ake kaiwa bisa al'ada.

Wannan abin goyo dai akan samar da shi daga fatar akuya da bunsuru ban da ta rago, kuma uwar miji ke samar da ita ta samu fatarta ta gyara har sai an yi haihuwa.

Ya na da sauki ga al'ummar kauyika na Abzinawa ga tsafta ga mutanen da ke zaune a wuraren da ba a cika samun ruwa ba. Yaro na dafe a ciki tsawon lokaci.

Har kwanan gobe Abzinawa ba su yada al'adunsu ba duk lokacin da su ka samu sabga ta haihuwa ko aure.