1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ECOWAS ta dage wa Nijar takunkumi

Abdourahamane Hassane
February 24, 2024

Shugabannin kasashe mambobin kungiyar ECOWAS sun yanke shawarar dage wani bangare na takunkumin da suka kakaba wa Nijar, in ji shugaban kungiyar Bola Ahmed Tinubu

https://p.dw.com/p/4cq5N
Hoto: Kola Sulaimon/AFP

 ECOWAS ta yanke shawarar dagewa ba tare da bata lokaci ba wasu daga cikin takunkuman da ta kakaba wa Nijar tun bayan kwace mulki a Yamai da gwamnatin soja ta hambarar da zababben shugaban kasar Mohamed Bazoum a watan Yuli. Za a sake bude iyakokin da sararin samaniya, a cewar sanarwar a karshen babban taron shugabannin   kasashen ECOWAS.