DW zata ba da taimakon rediyoyi ga lardin Aceh | Siyasa | DW | 05.01.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

DW zata ba da taimakon rediyoyi ga lardin Aceh

Tashar DW ta tsayar da shawarar gabatar da taimakon sake gina tashoshin rediyo da kuma raba kananan rediyoyi ga mazauna lardin Aceh da ambaliyar ruwa tayi kaca-kaca da shi a kasar Indonesiya

Tun bayan da aka samu rahoton farko a game da ambaliyar tekun da ta rutsa da lardin Aceh a kasar Indonesiya ayyuka suka fara kaiwa iya wuya ga ‚yan jarida dake aiki a sashen harshen Indonesiyan a nan Deutsche Welle. A cikin shirye-shiryen da yake gabatarwa a kullu-yaumin, sashen kan yi bayani dalla-dalla a game da halin da ake ciki a yankunan da bala’in ya shafa a kudu da kuma kudu-maso-gabacin Asiya. A irin wannan hali kuwa mutum na bukatar wani da zai rika tuntubarsa akai-akai. Amma da yawa daga cikin gidajen rediyon dake hulda da Deutsche Welle a lardin Aceh ba a jin duriyarsu. Bisa ga dukikannin alamu kuwa ambaliyar ruwan ce tayi awon gaba da su. A yankunan da bala’in ya fi tsamari mutane ba su da ikon samun bayanai da suke bukata domin kare makomar rayuwarsu, lamarin dake dada jefa su cikin mawuyacin hali na kaka-nika-yi. Wadannan mutanen basu da wata masaniya a game da irin barnar da ambaliyar tayi da kuma ire-iren kayan taimakon dake kan hanya zuwa gare su. Kazalika ba su da ikon samun wani bayani dangane da cututtukan dake barazanar yaduwa tsakaninsu. A sakamakon haka tashar Deutsche Welle ta tsayar da shawarar taimakawa wajen sake gina wadannan tashoshi na rediyo. A halin yanzu haka wata tashar rediyo dake hulda da DW a birnin Jakarta ta tura wata tawaga bin bahasi domin nemo cikakken bayani a game da ake bukata domin sake gina ko da tashoshi guda biyu ne a cikin gaggawa. Ita ma DW ta tura daya daga cikin ma'aikatanta na sashen harshen Indonesiya domin ziyarar ganin ido a yankunan da lamarin ya shafa da kuma tantance irin abubuwan da ake bukata da kuma gudummawar da tashar zata iya bayarwa akan manufa. A daura da haka an gabatar da matakin tara ‚yan kananan rediyoyi domin rabawa a cikin hamzari a tsakanin mutane a yankunan da bala’in ya rutsa dasu ta yadda akalla zasu rika samun rahotanni da sauraron labarai. Tare da wannan mataki DW ke fatan tabbatarwa da mutanen da tsautsayin ya rutsa da su cewar ba a manta da makomar rayuwarsu ba.