1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

DW ta bukaci bude reshenta da Masar ta toshe

August 17, 2017

Mahukunta a kasar Masar sun toshe wata kafar sadarwa ta intanet mallakin tashar DW wato Qantara.de. ba tare da sun bada wani gargadi ba.

https://p.dw.com/p/2iQxI
Qantara qantara.de Logo 1024 x 576

Ita dai kafar sadarwa da ke zama wata mujalla a yanar ta Intanet, tana taka muhimmiyar rawa a tattaunawa da duniyar Musulmi cikin harsunan Jamusanci da Ingilishi da kuma Larabci. Kalmar Qantara dai kalma ce ta larabci da ke nufin gada. Editocin mujallar ta intanet na mayar da hankali kan batutuwan siyasa da al'adu da kuma zamantakewar al'umma. Kafa ce kuma da ke ba wa jama'a damar fadin albarkacin bakinsu da mutunta juna.

Tuni dai kakakin tashar DW Christoph Jumpelt ya yi kira ga mahukuntan na Masar da su sake bude kafar sadarwa ba tare da wani bata lokaci ba. Tun a shekarar 2015 hukumomi a Masar ke sanya ido kan ayyukan tashar DW.