1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

DW – Labarai masu daukar hankali ga Gwarzayen Jama‘a

PInado Abdu-WabaJune 24, 2015

Ku ba mu labarin mutanen da ke kawo sauyi mai ma’ana a al’ummominku, domin samun kyaututtuka, wadanda suka hada har da kwamfutar tafi da gidanka, wato „tablet“.

https://p.dw.com/p/1Fmo6
Local Heroes TITELMOTIV HAUSSA
Hoto: DW

DW na goyon bayan gwarzayen jama‘a. Mutane wadanda ke nazarin batutuwan da suka shafi duniya, su fasara, su sake dubawa, sannan su samar da sabbin dabarun da za su kawo sauki. Wadanda ke samar da dokoki a maimakon aiki da wadanda ke nan, wadanda ke bai wa jama’a karfin gwiwa a maimakon karyawa. Muna tare da su, kuma aikinmu ne mu ba su irin labarai da bayanan da za su taimaka musu wajen gina rayuwarsu.

Wasu daga cikin labaran DW na gwarzayen jama‘a:

- A manta ba ya a gina gaba
- Tasirin maharba ga tsaro ba farautan kawai ba
- Wasannin motsa jiki hanyar sasantawa
- Ilimin kimiya ga marasa galihu
Akwai karin bayani kan gwarzayen jama’a na DW a sabuwar tasharmu ta Turanci a dw.com/localheroes

Ba tare da bata lokaci ba – Bayyana mana labarin gwarzayenku yanzu!

Muna so mu ji labarin wadanda ke kawo sauyi a al’ummominku. Misali, suna neman hanyoyin samar da magunguna a al’umma ne? Ko kuma suna fafutukar ganin wani kamfani ya samar wa jama’a aikin yi? Gwarzaye sukan dauki kowace irin suffa – Muna so mu ji labaranku mu kuma bayyana wa duniya wadannan gwarzaye naku.


Ku cike Ko kuma ku shiga dandalin sada zumuntarmu a shafinmu na Facebook don aiko mana da labarinku.
Za a zabi wadanda suka yi nasara daga duk wadanda suka cika sharudda. Wadanda suka turo labarai ba su da ‘yancin shigar da kara kotu ko da ba su yi nasara ba. Ya kamata a kammala turo sakonni ranar 19 ga watan Yulin 2015.


Kyaututtuka
- Na farko: Na’urar „tablet“ da wasu karin kyaututtuka
- Na biyu da na uku : Na’urar sauraron sauti ta Ipod da wasu karin kyaututtuka
- Kyauta ta karfafa gwiwa : kyauta daya daga cikin bakwan da aka tanadar wa gwarzayen jama‘a