DW a kwamitin al′adu na majalisar dokokin taraiya | Zamantakewa | DW | 29.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

DW a kwamitin al'adu na majalisar dokokin taraiya

Tashar Deutsche Welle ta sami goyon baya ga aiyukan ta daga wakilan majalisar dokokin taraiya ta Bundestag

Shugaban tashar DW, Erik Bettermann

Shugaban tashar DW, Erik Bettermann

Tashar DW, ba ta gwamnati bace, amma tasha ce mai cikakken yancin kanta. To duk da haka, a matsayin ta na tashar dake aiki da dokokin da suka shafi tashoshin yada labarai na jama’a, tana samun kudaden tafiyar da aiyukan ta ne daga hukumomi na kasa, saboda haka ma take karkashin kulawar majalisar dokoki ta taraiya. Ko da shike tashar ta DW, wajibi ne ta rika yiwa majalisar bayanin yadda take kashe wadannan kudade da take samu, amma majalisar bata da ikon yin katsalandan a shirye-shiryen da tashar take gabatarwa masu sauraron ta.

Dokokin da suka kafa DW, sun wajabtawa tashar, dake watsa shirye-shiryen ta zuwa ketare ta rika gabatarwa majalisar ta taraiya tsarin aiyukan ta sau daya a ko wane shekaru hudu. Rahoton ta na baya-bayan nan, shine wanda ya shafi shekara ta 2007 zuwa shekara ta 2010, wanda kuma bayan muhawara, majalisar zata amincve dashi gobe Jumma’a. Tun kafin haka, sai da kwamitin al’adu na majalisar ya tattauna kann wannan rahoto ranar Laraba.

Shugaban tashar ta DW, Erik Bettermann yana iya baiyana farin cikin sa ga sakamakon tattaunawar da aka yi ya zuwa yanzu. Shirin aiyukan tashar da ya gabatar har ya zuwa shekara ta 2010, ya sami karbuwa da amincewa daga dukkanin wakilai na jam’iyu dabam dabam a kwamitin al’adu na majalisar dokokin ta taraiya. Karkashin wannan tsari, yankunan da za’a fi maida hankali kansu a fannin siyasa, sune gabas ta tsakiya, kudu maso gabashi da gabashin Turai. Kazalika, za’a maida hankali ga duniyar Larabawa dea Iran da yankin Asiya.

A kasashen Iran da Vietnam, za’a bude shafunan Internet cikin harsuna na wadannan kasashe biyu, sa’annan a kasashen Larabawa za’a karfafa muhimmancin DW, ta hanyar fadada shirye-shiryen television daga awa ukku a rana yanzu zuwa awa shidda a kullum. Shugaban tashar ta DW, Erik Bettermann yace:

Idan a shekara mai zuwa muka sami nasarar samun wasu kudade, muna ganin wata dama, ta shigar da karin kudi daga asusun mu, domin fadada shirye-shiryen television na harshen Larabci har zuwa misalin awa goma sha biyu a kullum.

A yunkurin tabbatar da ganin an sami nasarar wannan shiri er, ya sanya tashar ta DW ta nemi karin kudi misalin Euro miliyan hudu daga gwamnatin taraiya, duk kuwa da ganin cewar gwamnatin ta rika rage yawan kasafin da ta ke baiwa tashar ne tun daga shekarun baya. Kwamitin al’adu na majalisar dokokin taraiya ya baiyana goyon bayan sag a dukkanin bukatun da tashar ta DW ta gabatar domin tafiyar da aiyukan ta, kamar yadda shugaban kwamitin, Hans-Joachim Otto, na jam’iyar FDP ya nunar, ko da shike ya kuma baiyana bakin cikin cewar tashar ba zata sami karin kudi kamar yadda ta nema ba.

Yace ina ganin a game da tashar DW, mun kawo iyakar kudaden da zamu iya ware mata. Tashar ta bunkasa aiykan da take gudahnarwa, godiya ta tabbata ga dukkanin ma’aikatan ta da darekta-janar na tashar da kuma shugaban ma’aikata. To amma idan kuma har muna bukatar aiyukan tashar su fi na yanzu kyau da armashi, wajibi ne mu kuma yarda da cewwar tana bukatar karin kudi.

Darekta-janar Erik Bettermann yace karin kudin da aka nema, ba saboda fadada shirye-shiryen sashen Larabci ne kawai ba, amma har saboda kyattata na’urori ne na watsa shirye-shirye, dake bukatar jari na Euro miliyoyi dubbai.

Yar majalisar dokoki daga jam’iyar Greens, Uschi Eid tace karancin kudi ko kuma hadin kann da ya zama tilas, tsakanin DW da tashoshi na cikin gida, kamar ARD da ZDF, bai kakata ya sanya a rage, ko a ki maida hankali ga sauran yankunan da tashar take watsa shirye-shiryen zuwa garesu ba, misali kudancin Amerika ko nahiyar Afrika, kudu da hamadar Sahara. Eid tace:

Akwai yankuna na nahiyar Afrika, inda babu yancin kafofin yada labarai, inda tashoshi da kafofin yada labarai na hukuma babu abin da suke yi in banda karkaatar da zukatan jama’a zuwa garesu. A irin wadannan kasashe ana bukatar yantattun hanyoyi da jama’a zasu rika samun labarai daga garesu.

Shugaban tashar ta DW, Erik Bettermann yayi alkawarin cewar babu wani bangare ko yanki na duniya da tashar zata yi shakulatin bangaro dashi. Hakan ya baiyana dukkanin wakilan kwamitin na majalisar dokoki suka gamsu, suka kuma baiyana goyon bayan su ga tsarin da ya gabatar.